
Asalin hoton, Getty Images
Manchester United ta tashi 2-2 da Leeds United a kwantan Premier League ranar Laraba a Old Trafford.
Cikin wadanda suka ci wa United kwallo har da Marcus Rashford, wanda ya zura na 20 a dukkan fafatawa a bana.
Haka kuma dan kwallon tawagar Ingila ya ci na 12 kenan tun bayan da aka kammala gasar kofin duniya a Qatar.
Rashford mai shekara 25 ya ci kwallo na shida a jere a Old Trafford a Premier League, bayan Wayne Rooney mai takwas a tsakanin Afirilun 2012.
Dan wasan tawagar Ingila ya fara cin kwallo ana gama gasar kofin duniya ranar Laraba 21 ga watan Disambar 2022 a Carabao Cup da United ta ci Burnley 2-0.
Rashford ya zura takwas a raga a Premier da uku a Carabao Cup da daya a FA Cup. tun bayan da aka gama gasar kofin duniya a Qatar.
United ta ci gaba da zama a mataki na uku a teburin Premier League mai maki 43 da tazarar biyu tsakaninta da Manchester City ta biyu.
Arsenal ce ke jan ragamar teburin babbar gasar tamaula ta Ingila ta kakar nan da maki 50.
Ranar Lahadi United za ta ziyarci Elland Road, domin buga wasa na biyu a Premier League da Leeds United.
Ranar Litinin leeds ta kori Jesse Marsch, wanda ya ja ragamar kungiyar kasa da shekara daya.
Bayan da Leeds ta tashi 2-2 da United a Old Trafford ta koma ta 16 daga mataki na 17 da makinta 19.
Jerin ‘yan wasan da suka ci kwallaye da yawa, bayan gasar kofin duniya
- Marcus Rashford Manchester United
- Erling Haaland Manchester City 8
- Harry Kane Tottenham 6
- Riyad Mahrez Manchester City 6
- Eddie Nketiah Arsenal 6