Ba Wanda Ya Tilasta Muku Siyan Kamfanin wutar Lantarki – FasholaMinistan Ayyuka da hasken wutar lantarki, Babatunde Fashola ya caccaki wadanda suka sayi kamfanin hasken wutar lantarki na ƙasa bayan sun kawo kuka kan rashin samun haɗin kai daga masu amfani da hasken wutar lantarki.

Ministan ya ja hankalin waɗannan kamfanoni wadanda a halin yanzu aka damkawa harkar wutar lantarki kan cewa har yanzu sun kasa zuba jari wajen inganta hasken wutar kamar yadda aka yi yarjejeniya da su kafin a yi masu gwanjon kamfanin.

Game da koken da kamfanonin suka gabatar kan cewa mafi yawan kayayyakin kamfanin hasken wutar lantarki sun tsufa, Ministan ya ƙalubalance su kan cewa babu wanda ya tilasta su sayen kamfanin sannan kuma kafin su sayi kamfani sun rigaya sun san halin da yake ciki.

You may also like