Ba Wanda Zan Marawa Baya A Zaɓen 2019 – Obasanjo


Tsohon Shugaban Kasa, Cif Olusegun Obasonjo ya jaddada cewa ba zai marawa kowane dan takara a zaben 2019 ba a maimakon haka zai ci gaba da kasancewa cikin iyayen kasa.

A makon da ya gabata ne, Obasonjo ya rubutawa Shugaba Buhar wata wasika inda ya caccake shi sannan kuma ya neme shi kan ya jingine batun sake tsayawa takara. Tsohon Shugaban ya kuma kafa wata kungiyar gwagwarmaya wadda aka yi zaton za ta rikide ta koma jam’iyyar siyasa don kawar da gwamnatin Buhari.

You may also like