
Asalin hoton, Getty Images
Pep Guardiola ya ce ba wani siddabaru yake yi ba a Manchester City da har ya lashe Champions League a karon farko.
City ta dauki Premier League da FA Cup a bara, wadda ta zama ta uku a Ingila da ta lashe kofi uku, wadda ta ci Inter Milan 1-0 a Champions League a wasan karshe.
City za ta fara kare kofin da ta dauka a bara da yin wasan farko a cikin rukuni ranar Talata, inda za ta karbi bakuncin Red Star Belgrade a Champions League.
”Abu ne mai sauki. Da zarar ka dauki kofin farko hanya ta buɗe” in ji Guardiola.
”A kungiyarmu lashe Champions League abin al’ajabi ne, amma idan ka yi duba na tsanaki, kungiyoyi nawa ne suka dauki kofi daya?
”Ba wata dabara da muka muna ta lashe kofin nan, amma muna alfahari da rawar da muka taka da tarihin da muka kafa.”
Kociyan na City ya ce bai tsaye sake kallon wasan da suka doke Inter Milan ba da suka lashe Champions League, wanda Rodri ne ya ci kwallon daya tilo.
”Ban kalli wasan ba ko kadan,” kamar yadda ya sanar.
Dan kwallon tawagar Ingila, Kyle Walker ya ce City, wadda take ta daya a Premier League da lashe dukkan wasa biyar, ba za ta gaza ba kan kwazon da ta yi a bara.
Bayan kungiyar Serbia, Red Star Belgrade, City za ta buga wasannin cikin rukuni a Champions League da RB Leipzig ta Jamus da Young Boys ta Switzerland.