
Asalin hoton, Getty Images
Ƴan Najeriya sun yi ta mayar da martanin kan sauyin matakin babban bankin ƙasar, CBN na ƙara yawan kuɗaden da za a iya cira a banki.
Lamarin ya yi wa wasu daɗi amma da dama na ganin sauyin matakin a matsayin “La ba a sa”, wato babu yabo babu fallasa.
A ranar Laraba ne CBN ya sanar da cewa ya ƙara yawan kuɗaɗen da ɗaiɗaikun mutane za su iya cirewa a banki daga Naira 100,000 a sati zuwa 500,000, yayin da kamfanoni za su iya cire Naira miliyan biyar maimakon N500,000 da aka sanar tun farko.
Sauyin na CBN na zuwa ne bayan matsin lamba da sukar da ya sha daga ƴan ƙasar da dama, ciki har da majalisar wakilai da kuma masana.
Cikin waɗanda suka bayyana jin daɗinsu da sauyin har da masu sana’ar POS da kuma masu tsokaci a shafukan BBC Hausa na sada zumunta.
Wani mai sana’ar POS a jihar Kano da BBC ta ji ta bakinsa ya ce sauyin da kaa samu na ƙara yawan kuɗin da za a dinga cira a bankin “ya ɗan” faranta musu rai.
“Amma ba dai sosai ba kamar yadda ake yi da. Mu da a matsayinmu na ejen muna cire kudi a banki ba ƙayyadewa, ko nawa ne muna cira.
“Sai dai duk da haka ƙarin da aka yi ɗin zuwa naira 500,000 daga N100,000 shi ma ba laifi, amma da so samu ne a ƙara ko da zuwa miliyan ɗaya ne a sati.
Mutumin ya ce a duk rana yana hada-hadar kudi har naira miliyan ɗaya ko sama da haka.
Shi ma wani mai POS din ya ce ya ji dadi da aka samu ƙarin, “saboda naira dubu ɗarin da aka ce za mu dinga karɓa a sati da farko to zai sa kasuwancinmu ya samu tangarɗa.
“Wannan ƙarin ya yi mana, amma da so samu ne ko miliyan ɗaya a mayar da shi, amma hakan ma ba laifi,” ya ce.
Ba a bar ƴan soshiyal midiya a baya ba
Mutum sama da 1,100 ne suka yi tsoakaci a kan labarin a shafin BBC Hausa na Facebook bayan wallafa shi a ranar Laraba.
Kuma ga abin da wasu daga cikinsu ke cewa:
Aminu Salihu ya ce: Idan har daman don cigaban tattalin arzikin kasa aka yi wannan tsari, me yasa yanzu aka sanja?
Ko kuma daman batun da ake cewa saboda fakon ƴan siyasa ne aka yi ba wai don cigaban kasa kamar ydda aka ambata da fari ba!”
Abbakar Sani Mamman Yanduna: Ya ce Masha Allah! Wannan doka ta yi daidai. Amma dai kar mu manta muna tunawa da cewa wannan abin ana yi ne don talakawan kasar nan da kuma samun kyakkyawan tsaro musamman a arewa. Allah ya sa mu dace. Ameen.”
Abdulrahman Sanusi Ahmad ya ce: “To Allah ya kyauta. Amma akwai Rina a kaba kam. CBN ya yi amai ya lashe kenan kan matakinsa na ƙayyade yawan kuɗaɗen da za a dinga cirewa daga bankuna a ƙasar.
“Dama ya bar tsarin da ya yi na farkon, don hakan zai ba da damar sayen ƙuri’u a hannaun al’umma.”
Salisu Mai Shinkafa Song ya ce: “Hakika wannan matakin da Babban bankin Nigeria CBN ya dauka na kara yawan adadin kudin da mutane za su cire daga asusunsu na banki ya yi dai dai. Abin da ya rage shi ne babban bankin ya kara wa’adin da za dai na karba tsofaffin kudi kawai.”
Tasi’u Aminu Muh’d ya ce: CBN ya kyauta amma sabbin kuɗin da aka buga sun yi kaɗan tabbas idan aka tafi a haka mutane za su tafka asara domin akwai mutane da yawa da har yanzu ba su taɓa ganin waɗannan sababbin kuɗin ba.”
Tsokacin masana
To sai dai duk da sauya matakin, CBN bai janye batun cewa duk wanda zai cire kuɗaɗen da suka haura adadin da aka kayyade ba a mako saboda dalilai masu ƙarfi, to sai an caji kashi 3 cikin 100 ga ɗaiɗaikun mutane da kuma kashi 5 cikin 100 ga kamfanoni.
Kan hakan ne BBC Hausa ta tuntubi Dr Shamsudden Muhammad na Jami’ar Bayero Kano, don jin abin da zai ce kan mi’ara koma bayan da CBN ya yi.
Ya ce: “Ƙara yawan kuɗaden da za a iya cirewa a bankin zai taimaki masu POS da attajiranmu na ƙauye da ba su saba da mu’amala ta banki ba.
“Hakan zai a kasuwancinsu ya ɗore, wanda ba don sauyin ba da sai ya durƙushe, kuma hakan zai iya janyo ƙaruwar rashin aikin yi a ƙasa da kuma talauci.
“Amma inda matsalar take shi ne, wannan na nuna cewa ana yin dokoki a CBN ba tare da dogon nazari ba, tun da zai kai ga a yi doka bayan sati ɗaya ko biyu a canja ta,” in ji masanin.
Bugu-da-ƙari Dr Shamsuddeen ya ce ɗaukar irin wannan mataki yana ƙara haɗarin kasuwanci, inda zai riƙa korar masu zuba jari, musamman na ƙasashen waje.
“Saboda muddin babban bankin ƙasa yana fito da dokar kuɗi kuma yana warwarewa, to wannan yana nuna akwai haɗari babba ga manya-manyan kasuwanci wanda ke naso zuwa ƙanana,” a cewar Dr Shamsuddeen.