
Asalin hoton, Getty Images
Sabon kuɗin zai nuna al’ada da tarihin mutanen Australia na ainihi.
Ba za a sanya hoton Sarki Charles na uku ba a jikin takardar dalar Australia mai biyar, in ji babban bankin ƙasar.
Sabon kuɗin da za a sauya zai karrama a’adu da tarihin ‘yan asalin Australia na ainihi, in ji babban bankin.
Za a sanya hoton marigayiya Queen Elizabeth III a jikin sabon kuɗin na dala mai biyar.
Mutuwar Sarauniyar a bara, ta janyo muhawara kan ko Australia za ta ci gaba da tafiya kan tsarin mulukiya.
“Mataki kwamitin ƙolin babban bankin na zuwa ne tattaunawar da suka yi da gwamnati, wadda ta nuna goyon bayanta ga sauyin kuɗi,” kamar yadda yake cikin wata sanarwar da babban bankin ya fitar.
“ Da farko bankin sai ya fara tuntuɓar mutanen Australia kan sauya takardar dala biyar ɗin. Kuma sabon kuɗin zai kwashe shekaru kan a buga shi a fitar da shi.
“A gefe guda kuma, za a ci gaba da amfani da takardar dala biyar a faɗin ƙasar. Kuma za a ci gaba da amfani da ita har bayan an buga sabbin kuɗin,” kamar yadda ya bayyana.
Dala biyar ɗin ita kaɗaice kuɗin Australia da ke ɗauke da hoton sarakan Birtaniya. Kuma akwai hoton marigayiya sarauniya a hoton silallan kasar, duk da dai Australia na shirin sanya mutum-mutumin Sarki Charles III.
Babban bankin ya shaida wa BBC cewa bai sanya lokacin da zai nuna sabuwar takardar dalar ba.
‘Yan siyasa da shugabannin al’umma sun yi maraba da wannan mataki.
“Wannan wata babbar nasara ce wadda aka samu tun daga tushe, Ƙasa ta farko da mutanenta suka yi yaƙi domin ceto ta daga mulkin mallaka,” in ji Sanata Lidia Thorpa.
Mutanen farko da suka zauna a Australia sun rayu ne kimanin shekara 65,000 gabanin zuwan turawan mulkin mallakar Birtaniya, kamar yadda ƙididdiga ta nuna.
Asalin hoton, Getty Images
Sarki Charles ya zama satki ne bayan mutuwar mahaifiyarsa a watan Satumba.
Kuma shi ne shugaban Australia da New Zealand da wasu ƙasashe 12 na rainon Ingila waɗanda ke wajen masarautar Birtaniya. Matsayinsa ya fi ƙarfi a wuraren gudanar da bukukuwa.
A duka kuɗaɗen Australia ba a rasa sa hoton aƙalla basarake ɗaya na Birtaniya a duk lokacin da za a buga su.
A watan Satumba ne ƙasar ta ce ba za a maye hoton Sarauniya ba nan datke da hoton Sarki Charles a jikin dalarta mai biyar ba, wataƙila sai dai a mayeta da wani fitaccen daga Australia.