Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osibanjo ya tabbatar da cewa gwamnati ba ta da shirin karin kudin hasken wutar lantarki a yanzu kamar yadda kamfanonin samar da wutar lantarki suka nema.
Sai dai kuma Mataimakin Shugaban ya nuna cewa dole nan gaba a yi karin kudin amma a yanzu gwamnati na kokarin ganin cewa ta samar da tallafi ga kamfanonin da suka sayi kamfanin wutar lantarki na kasa don ganin sun inganta harkar samar da wutar lantarki.