
Asalin hoton, Getty Images
Julius Malema
Jam’iyyar adawa a Afirka ta kudu EFF, ta ce shugaban Rasha Vladmir Putin na da damar ziyarar ƙasar ta Afirka duk kuwa da cewa Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta bayar da sammacin kama shi.
Kotun ta ICC na zargin shugaba Putin da laifukan yaƙi, waɗanda suka haɗa da garkuwa da yara ƴan asalin Ukraine, a mamayen da Rashar ke yi wa ƙasar.
Ana sa ran Mr Putin zai kai ziyara Afirka ta kudu a watan Agusta domin halartar taron ƙungiyar Brics(Brazil, Russia, India da Afirka ta kudu).
Jagoran jam’iyyar EFF, Julius Malema a ranar Alhamis ya ce babu wanda zai kama Vladmir Putin a Afirka ta kudu, kasancewar Rasha ta taimaka sosai wajen ƴanta ƙasar.
Mr Malema ya buƙaci gwamnatin ƙasar ta Afirka ta kudu da kada matsi daga ICC ya sanya ta yi yunƙurin kama Putin, abin da ya bayyana a matsayin ‘munafinci.’
Ya ce “Muna maraba da Putin. Babu wanda ya isa ya kama shi. Idan ta kama, za mu je har filin jirgi mu taho da shi zuwa wurin da zai yi jawabi, idan ya gama jawabi mu sake raka shi filin jirgi.”
Malema ya ƙara da cewa “mun san abokanmu. Mun san waɗanda suka ƴanta mu. Mun san waɗanda suka taimaka mana.”
Afirka ta kudu dai na da hulɗar dangantaka mai ƙarfi da Rasha duk da suka daga ƙasashen yamma.
A watan da ya gabata sojojin ruwa na Afirka ta kudu sun yi atisaye tare da na Rasha a gaɓar teku da ke iyaka da Afirka ta kudun.
Haka nan ƙasar ta ƙaurace wa ƙuri’ar da aka kaɗa a zaurten Majalisar ɗinkin duniya ta yin tir da mamayen Rasha a Ukraine.
A 2015 an soki Afirka ta kudu saboda ƙin kama shugaban Sudan Omar al-Bshir a ƙasar duk da umurnin ICC na kama shi.