‘Ba za mu shiga zaben fitar da gwani na gwamna a APC a Taraba da za a yi ba’APC

Asalin hoton, OTHER

Yayin da a ranar 10 ga watan Fabrairun 2023, ne za a yi zaɓen fitar da gwani, don zaɓo mutumin da zai yi wa jam’iyyar APC takarar gwamna a jihar Taraba da ke arewa maso gabashin Najeriya, da yawan masu neman takarar a jihar sun ce ba za su shiga zaɓen ba.

‘Yan takarar dai sun yi zargin cewa ba a sanar da su game da zaɓen fitar da gwanin ba, sannan an cika Jalingo da sojoji don a razana magoya bayansu.

Matakin da ‘yan takarar suka dauka na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan Kotun Ƙoli ta kori Sanata Emmanuel Bwacha, a matsayin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar ta Taraba.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like