
Asalin hoton, Getty Images
Ukraine na neman taimakon jiragen yaƙi domin ƙarfafa sojojinta da ke ci gaba da gwabza faɗa da Rasha
Shugaban Amurka Joe Biden, ya ce ba zai tura jiragen yaƙin F-16 zuwa Ukraine ba, duk da kiraye-kirayen da jami’an Ukraine din ke yi na buƙatar ƙarin tallafin jiragen yaƙi.
Lokacin da wani ɗan jarida ya tambaye shi a ranar Litinin cewa ko Amurka za ta tura jiragen yaƙi, sai ya ce a’a.
Kalamansa na zuwa ne kwana guda bayan da shugaban gwamnatin Jamus shi ma ya ce ba za su tura jiragen yaƙin ba.
Ukraine ta daɗe tana rokon ƙawayenta su tallafa mata da jiragen yaƙi domin samun damar kare sararin samaniyarta a ci gaba da gwabza faɗa da take yi da Rasha.
Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky da manyan jami’an sojin ƙasar sun ce babu wani abu mara kyau a taimakon na soji – sai dai Amurka da ƙawayenta na tsoron hakan zai iya janyo babbar matsala da ƙasar Rasha mai makamin nukiliya.
Ana kallon jiragen yaƙin F-16 da Amurka ta ƙera a matsayin masu karko a duniya wanda ƙasashe da dama ke amfani da su, kamar Belgium da Pakistan.
Za su iya kawo babbar sauyi kan jiragen yaƙin tarayyar Soviet na MiGs – da Ukraine ke amfani da su a yanzu, waɗanda aka ƙera kafin ƙasar ta ayyana samun ‘yancin kai daga tarayyar a shekarar 1991.
Sai dai, mista Biden ya sha yin watsi da rokon Ukraine na aika mata jiragen yaƙi, inda maimakon hakan sai ya karkatar da hankali ta wajen bayar da taimakon soji.
A makon da ya gabata, Amurka ta sanar da cewa za ta aika wa Kyiv tankokin yaƙi na Abrams guda 31, inda ta yi amai ta lashe a matsayarta a baya kan lamarin.
Birtaniya da Jamus su ma sun yi alkawarin bayar da taimakon tankokin yaki.
Mataimakin ministan harkokin wajen Ukraine, Andriy Melnyk, ya yi maraba da matakin, amma ya buƙaci ƙawayen nasu da su kulla “ƙawancen jiragen yaki” wanda zai samar wa Ukraine da jiragen yaƙi daga ƙawayenta na Turai.
A wata tattaunawa a ranar Lahadi, shugaban gwamnatin Jamus, ya ce abin kamar da wasa idan aka yi batun tura wa Ukraine taimakon soji idan aka duba cewa gwamnatinsa ta amince da aika tankokin yaƙi ne kawai.
Olaf Scholz ya faɗa wa jaridar ƙasar Tagesspiegel cewa ƙawancen sojin Nato ba faɗa da Ukraine suke yi ba, kuma ba za su bar “lamurra su tabarbare ba”.
Da yake magana a ranar Litinin, shugaban ƙasar Faransa, Emmanuel Macon, ya ce ba a kai ga yanke shawara kan komai”, kan batun bai wa Ukraine taimakon soji ba.
Sai dai, ya nanata cewa ba za su yi abin da zai ƙara rura wutar rikicin ba ko kuma rage batun kare kanta.
Ministan tsaron Ukraine, Oleksii Reznikov, ya je Paris babban birnin Faransa a halin yanzu, inda ake sa ran zai tattauna kan batun da manyan jami’an gwamnatin Faransa.
Ita ma Poland – da ta ƙasance ƙawar Ukraine – ta jingine batun tura mata jiragen yaƙi.
Sai dai, firaministan ƙasar ta Poland, Mateusz Morawiecki, ya ce duk wani yunkuri kan buƙatar, zai yi nasara ne kawai muddin aka samu haɗin kai tsakanin mambobin Nato.
Andriy Yermak, shugaba a ofishin shugaba Zelensky, ya ce Ukraine ta samu bayanai masu kyau daga birnin Warsaw.
Moscow ta sha zargin Nato na kai mata hari ta hanyar amfani da mambobinta, wadanda suka hada da Amurka da Jamus, inda suke ɗari-ɗarin tura taimakon sojin da zai iya janyo kazancewar faɗa da ake gwabzawa a Ukraine.