Ba Za Muyi Rigista Ba Tunda Ba Kungiya Bace – ‘Yan Shi’aMabiya harkar ‘Islamic Movement of Nigeria’ ta mazhabar Shi’a, ta ce ba za ta yi rijista ba, domin kira take yi, ba kungiya ba ce.
Wani jami’in tafiyar, Barista Haruna Magashi ne ya bayyana hakan a wani taron sasanta rikicin ‘yan Shi’ah da ‘yan sanda, a jihar Kano.
Tun da farko, mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, Toluse O. Emmanuel ya nanata cewa matukar mutum ko kungiya suka nemi izinin yin ‘halartaccen’ taro, ba shakka ‘yan sanda za su ba su dama.
Barista Magashi ya koka a kan yadda mutane ke ‘shayin’ kusantarsu don jin abin da tafiyarsu ta kunsa daga bakinsu.

Wani mai gabatar da mukala a taron, Prince Ajayi Memaiyetan ya soki lamirin yadda ‘yan sanda ke amfani da bindiga don tarwatsa jerin gwanon ‘yan Shi’a.
Sai dai kuma wasu masu magana da dama a wurin taron, sun ce ba dai-dai ba ne yadda harka islamiyya ke gudanar da taro, ba tare da neman izinin hukuma ba.
Wannan dai wani matakin farko ne na tattaunawa kan rikicin ‘yan Shi’a da jami’an tsaro kuma ya samu wakilcin mabiya addinai daban-daban.

You may also like