Ba Zamu Bari a Sayar Da Kamfanonin Wutar Lantarki Ba – MajalisaBatun gyara wannan doka ta shekara 2005 da Kwamitin Kula da Harkokin Makamashi a Majalisar Wakilai ke son yi, ya samo asali ne akan wata bukata ta kungiyar Gwamnoni ta Kasa, wato NGF, inda suka nemi a samar da tsarin doka da zai fitar da yadda za a daidaita ayyukan samar da wutar lantarki a yakunan karkara.

Shugaban Kwamitin Magaji Da’u Aliyu ya ce a matsiyin Kwamitin Kula da Makamashi, akwai dokar kasa da ta banbanta da dokar da kungiyar gwamnonin Najeriya ke so da za ta ba su damar samar da wutar lantarki da rarraba ta a kasar ba.

Magaji ya ce akwai dokoki biyu da suka yi karo da na kundin tsarin mulkin kasa, ya kara da cewa, doka ta biyu ita ce a kasa. Magaji ya ce Kwamiti ya karbi dukan takardun kungiyoyi da na masu ruwa da tsaki da suka halarci taron kuma za su duba takardun sosai, sannan su yanke shawarar mataki na gaba da za‘a dauka tare da la’akari da inda kundin tsarin mulki ya fito kararra kan samar da wutar lantarki da sarrafa wutar.

Zaman Kwamitin Kula da Harkokin Makamashi a Majalisar Wakilan Najeriya3

Zaman Kwamitin Kula da Harkokin Makamashi a Majalisar Wakilan Najeriya3

Magaji ya kara da cewa ba za su bari a maimaita kwamacala da aka yi a baya wajen sayar da kamfanonin wutar lantarki ba, domin kudaden ba za su kirgu ba kuma ba za’a iya fadin su ba.

A lokacin da ya ke amsa tambayar ko Majalisar ba ta makara ba ganin cewa saura mata watanni kalilan ta nade tabarmarta? Wakilin Kakakin Majalisar Wakilai a taron, Abubakar Abdullahi Ahmed, ya ce ba a makara ba saboda aiki kadan ya rage a kammala gyaran dokar, kuma ba zai dauki lokaci ba.

Shi kuwa Karamin Ministan Wutar Lantarki, Goddy Jedy Agba, wanda ya halarci taron, ya yi tsokaci akan zaman yana cewa lallai an dade ana fama da wannan bangare na wutan lantarki, saboda haka zai yi ammana da gyara dokar da zai sa a samu daidaito a harkar tafiyar da wutar lantari a kasar, tun da gwamnati ta cire hannun ta a yawancin bangarorin tafiyar da harkar wutar lantari.

Agba ya ce kowa yana so a shawo kan matsalar wutar lantarki kuma an riga an dauki hanya.

Kwamitin Kula da Harkokin Makamashi a Majalisar Wakilan Najeriya 2

Kwamitin Kula da Harkokin Makamashi a Majalisar Wakilan Najeriya 2

Amma ga mai fashin baki a al’amuran yau da kullum kuma tsohon Mataimakin Shugaban Kungiyar Kwadago ta kasa Kwamred Isa Tijjani, yace yana ganin an dade ana irin wadannan tarruka na gyara dokoki, amma baya ganin tasirin su saboda wasu dalilai.

Kwamred Tijjani ya ce a ganinsa wannan Majalisa dai ta jeka na yi ka ne kawai, saboda duk abin da aka yi na almundahana sun sani, amma sun yi shiru, duk wani abu da ya shafi wutar lantarki sun sani amma sun yi shiru, ya ce akwai wuri ma da ko shara ba a yi ba amma sun yi shiru, duk abin da aka kawo ko ya yi wa talaka kyau ko bai yi ba sai majalisa ta yi shiru.

Abin jira a gani shi ne irin gyaran da Kwamitin Kula da Makamashi zai yi wa dokar da zai sa masu ruwa da tsaki su amince da ita saboda a yi wa fanin samar da wutar lantarki gyara na dindindin.

Saurari cikakken rahoton Medina Dauda:Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like