Ba Zan Amsa Gayyatar Majalisa Ba – Abdulmuminu Jibril


 

 

A yau Litinin ne ya kamata tsohon shugaban kwamitin kasafin kudin Majalisar Wakilai, Hon Abdulmumini Jibrin ya bayyana a gaban kwamitin da’a na majalisar, sai dai ya bayyana cewa ya yanke hukuncin ba zai masa gayyatar ba.

Hon Jibril ya bayyana haka ne a yayin da ya kira wani taron manema labarai a jiya Lahadi inda ya sanar da cewa ba zai mutunta gayyatar kwamitin ba.

Ya ce ya yanke shawarar hakan ne saboda ya riga ya gano cewa rashin adalci za’a yi masa a majalisar. Ya kara da cewa dalilinsa shi ne mutanen da za su jagorancin kwamitin ‘yan amshin shatan shugaban majalisar ne, Yakubu Dogara.

A makon jiya ne dai majalisar ta umarci kwamitin da ta binciki Hon. Abdulmumini Jibrin kan zargin yin kalaman bata suna ga majalisar kuma ta gayyaci dan majalisar da ya bayyana a gabanta a yau Litinin.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like