
Asalin hoton, Getty Images
Ɗan ƙwallon Faransa, Kylian Mbappe ya ce ba zai ‘ɓata lokaci ba kan masu abubuwan banza’ ba, bayan da aka tambaye shi game da abubuwan da golan Argentina, Emiliano Martinez ya yi masa a gasar cin kofin duniya.
“Murna saboda samun nasara ba wani abu ba ne a wuri na, ” Mbappe ya shaida wa gidan talabijin na RMC.
“Ba zan ɓata lokaci ba a kan abubuwan banza.”
Martinez, ya yi shaguɓe bayan Argentina ta samu galaba a gasar cin kofin duniya game da doke Faransa.
Mbappe, wanda ya zura ƙwallo uku a wasan ƙarshe ya ce wasan ba wai tsakaninsa da takwaransa na PSG Messi ba ne.
“Na yi magana da shi bayan wasan, kuma na taya shi murna,” in ji Mbappe.
Ɗan wasan mai shekara 24, ya lashe kyautar takalmin zinare saboda cin ƙwallo takwas a gasar da aka buga a Qatar.