Ba Zan Fito Takara Tare Da Ganduje Ba A Zaben 2019 – Mataimakin Gwamna Prof. Hafiz Abubakar Mataimakin Gwamnan jihar Kano Farfesa Hafizu Abubakar ya bayyana cewar ba zai yi takarar Gwamna tare da Abdullahi Umar Ganduje ba a matsayin mataimakinsa a zaben 2019 ba.

Farfesa Hafiz ya bayyana hakan ne a wani sauti da gidan radiyon Rahama dake jihar Kano ya watsa a jiya Litinin, inda aka jiyo Farfesa Hafizu yana nesanta kansa da duk wani yunkuri na sake yin takara tare da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a zaben 2019.

You may also like