Ba Zan Iya Cewa Ga Lokacin Da Nijeriya Za Ta Fita Daga Halin Tabarbarewar Tattalin Aziki Ba-Ministar Kudi


Ministar kudin  Nijeriya Misis Kemi Adeosun a wata hira da aka yi da ita jiya a Abuja, ta bayyana cewa ba ta da tabbacin lokacin da kasar nan za ta fita daga wannan hali na tabarbarewar tattalin arziki da ya kawo matsi da wahalar rayuwa ga da yawa ga mutanen kasar.
Ministar ta bayyana cewa fita daga tabarbarewar tattalin arziki da kasar nan ke ciki ya ta’allaka ne da ci gaban kasar, a saboda haka sai dai ta yi bayani kan hanyoyin da su ke bi don ciyar da kasar gaba, wanda shi ne zai yi sanadiyyar fitar da kasar daga halin da ta ke ciki.
Ta ci gaba da cewa, “Za ta iya yiwuwa kasar ta dau tsawon lokaci cikin halin tabarbarewar tattalin arziki, duk da kasancewar mun fara ganin alamu masu kyau daga harkokin noma da albarkatun kasa, sannan kuma muna bakin kokari wajen kawo sauyi a sauran bangarorin tattalin arziki. Da wannan na ke tabbatar mana da cewa lalle za mu fita daga wannan halin matsin.”
Idan dai ba mu manta ba, shugaban babban bankin Nijeriya CBN Mista Godwin Emefiele a makon da ya gabata ne ya ke bayyana cewa Nijeriya ta haye siradin tabarbarewar tattalin arziki, kuma daga karshen wannan shekara abubuwa za su fara daidaituwa.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like