Ba zan janye daga takara ba inji Trump


 

2015-11-21t191320z_2114450315_gf20000069032_rtrmadp_3_usa-election-trump_0

 

 

Dan takara karkashin jam’iyyar Republican Donald Trump ya ce ba zai janye takararsa ba duk da kira daga wasu jiga jigan jam’iyyar bayan gano wani hoton bidiyon da ya nuna shi yana furta wasu kalaman batsa.

Manyan ‘ya’yan jam’iyyar fiye da goma ne suka sanar da janye goyon bayansu  cikinsu har da abokin takararsa Mike Pence da ya bayyana rashin jin dadin shi bayan fallasar bidiyon.

A cikin bidiyon wanda aka dauka a shekarar 2005 kuma jaridar Washinton Post ta fallasa, Trump ya furta kalaman batsa na rayuwarshi  ta lalata da mata da kuma yadda  ya taba kokarin sumbatar wata matar aure..

Sai dai tuni Mr Trump ya fito ya nemi gafara a wani jawabinsa da aka yada ta kafar telebijin a ranar Asabar.

Trump ya ce ya yi nadama da kuskure kuma yana neman gafara amman yace ba gudu ba ja da baya a cigaba da takarar zama shugaban kasar Amurka, ya kuma ce yin hakan tamkar kunyata dubban magoya bayansa ne.

A wani lokaci yau Trump da ‘yar takara a karkashin jam’iyyar Demokrat Hillary Clinton zasu gudanar da mahawara zagaye na biyu.

You may also like