
Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP a Najeriya, Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce ba zai yi wa Gwamnan Kano mai jiran gado, Abba Kabir Yusuf, katsalandan ba a harkar tafi da mulki.
A wata hira da BBC, Kwankwaso, wanda shi ne jagoran jam’iyyar ta NNPP na kasa, ya ce idan gwamnan mai jiran gado ya nemi shawararsa zai ba shi.
Sai dai ya ce a matsayinsa na dan Kano zai rinka ankarar da gwamnatin a duk lokacin da ya ga an kauce hanya.
Jagoran jam’iyyar ta NNPP, ya ce “ Ai shi mulki ko mai shararka ne ka ba shi to ka koma waje daya in ya nemi shawararka ka bayar, idan kuwa bai nema ba sai ka yi shiru.”
Ya ce, abin da ya sani shi ne a lokacin da yake gwamna a Kano, da su Abba aka yi mulkin, su ne suka taimaka aka samu nasara.
Kwankwaso, ya ce, “ A yanzu na tabbata shirmen da Ganduje ya yi a Kano, ai Abba na tabbata ya wuce wannan, saboda haka ne ma muka zauna muka duba dukkannin mutanen namu muka dauki wanda muke ganin idan Allah Ya yarda in dai irin matsaloli na Ganduje ne ba za a samu ba.”
Tsohon gwaman, ya ce,” Dukkanninmu a jihar Kano muna farin ciki Allah Ya fitar da su, kuma muna addu’ar Allah Ya raka taki gona.”
Kwankwaso, ya ce abin da yake so a sani shi ne ”ko wanene yake mulkin Kano ko soja koma wanene ba za mu kyale shi ya yi rashin kyauta ba.”
Ya ce, “ Don haka ko Abba ke mulki ko ma waye duk wani abu da yake daidai za mu fada masa idan ma ba daidai ba ne za mu fada.”
Kwankwaso ya ce, shi abin da ya sani shi ne za a gyara duk wasu abubuwa da aka yi ba daidai ba a lokacin gwamnatin da ta gabata.
Ya ce, za a yi hakan ne don a gyara Kano ta yi kyau.