Ba zana bi Atiku zuwa PDP ba- Maman TarabaAisha Jummai Alhassan, Ministan Al’amuran Mata, kuma makusanciyar tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, ta karya ta hasashen da ake na cewa zata fice daga jam’iyar APC.

Ministar ta kuma bayyana biyayyarta ga shugaban kasa Muhammad Buhari inda tace “ina cikin kuma zan cigaba da kasancewa a cikin jam’iyar APC.”

A cikin watan Disamba ne, Atiku Abubakar,ya sauya sheka zuwa jam’iyar PDP.

A wancan lokaci anyi hasashen cewa, Alhassan da kuma wasu makusantan tsohon mataimakin shugaban kasar za subi sawunsa wajen ficewa daga APC zuwa PDP.

Tun farko cikin watan Satumba gabanin ficewar ta Atiku, ministar ta bayyana cewa zata goyi bayansa a zaɓen shekarar 2019 koda kuwa Buhari zai yi takara.

Amma acikin wata hira da tayi da jaridar Premium Times ministar tace babu wanda ya tilasta mata ficewa daga PDP, jam’iyar da a karkashinta ne ta zama sanata tace zata cigaba da zama a APC.

“Siyasa an gina tane akan ra’ayi, babu wanda ya tilasta mun ficewa daga jam’iyar PDP zuwa APC, saboda haka babu wanda zai tilasta min ficewa daga ita,”tace.

You may also like