Babachir ya kwana ɗaya a ofishin EFCC inda ake masa tambayoyi


Babachir David Lawal, tsohon sakataren gwamnatin tarayya yanzu haka yana hannun Hukumar Yaƙi Da Yiwa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati ta EFCC a ofishin hukumar dake Abuja.

Wata majiya tace Lawal ya isa ofishin EFCC da misalin ƙarfe 11 na ranar Laraba inda aka shiga yi masa tambayoyi.

Majiyar tace Lawal ya shafe daren jiya a ofishin hukumar yaƙi da yiwa tattalin arzikin kasar zagon ƙasa kuma an cigaba da yi masa tambayoyi a yau Alhamis.

Wannan cigaban da aka samu na zuwa ne sa’o’i 24 bayan wasikar da tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya rubuta wa shugaba Buhari inda a ciki yake zarginsa da boye mutanen dake jikinsa daga tuhuma kan aikata cin hanci da rashawa.

Lawal dai ya fara fuskantar rikici ne bayan da kwamitin majalisar dattawa ya zarge shi da bada kwangilar cire ciyawa ga wani kamfani da ake zargi mallakinsa ne karkashin shirin shugaban kasa kan  tallafawa mutanen da rikicin Boko Haram ya shafa a yankin Arewa maso Gabas.

Kimanin naira biliyan ₦2.5  ne suka yi ɓatan dabo a kwamitin da Lawal ke jagoranta.

A cikin kuɗin an yi zargin Lawal ya yi amfani da miliyan ₦570 wajen yanke ciyawa.

You may also like