Babban Bankin Najeriya Ya Ce Ba Zai Kara Wa’adin Sauya Kudi Ba
Wani bincike da Muryar Amurka ta gudanar na nuni da cewa, yawancin bankuna da ke Babban Birnin Tarayya Abuja suna sa sabbin kudade a na’urar su ta ATM amma kafin a ce kwabo sun kare, domin mutane suna layi tare da yin sammako domin cire kudi a na’urar.

Wani abu da ya dauki hankali kuma shine, ba a bada sabbin kudi akan kanta, amma ana karban tsoffin kudin.

A wasu jihohi na Arewa irin su Sokoto, Kan, Borno, Yobe da Katsina, labarin duka iri daya ne, a wasu lokuta ma ana samun mutane suna Jam’in sallah a cikin banki domin tsananin jira mai tsawon lokaci da suke yi saboda su canza kudaden su.

A hirar shi da Muryar Amurka, Sanata Kabir Ibrahim Gaya mai wakiltan Kano ta Kudu, yayi bayani cewa, yankunan sa na Shiyar Kano ta Kudu babu bankuna kuma a inda ake da bankunan ma, babu sabbin kudi a cikin su, saboda haka yake ganin ya kamata mahukunta su dauki mataki, domin ana ta rufe kasuwanni, matasa ‘yan kasuwa suna ta kokawa.

A bangaren Borno ta Kudu kuma, Sanata Mohammed Ali Ndume ne yayi korafi a madadin mutanen Jihar, inda ya ce yawancin al’umman Jihohin Arewa Maso gabas ba sa alaka da banki, kuma yanzu haka sun rufe shagunan su duka, domin suna tsoron karban tsofaffin kudi, gashi kuma babu sabbin a bankuna.

Ndume ya ce ya tuntubi lauyoyinsa akan matakan da zai dauka na tilasta wa bankin CBN ya kara wa’adin lokacin canjin kudin.

Masanin harkokin zamantakewan dan adam da gudanar da mulki kuma Malami a Jami’ar Abuja, Dokta Abdurrahman Abu Hamisu, ya yi tsokaci akan batun cewa, wannan tsari da gwamnati ta kawo na takura wa talaka ne, saboda haka yake kira akan a dauki darasi daga wasu kasashe da suke canjin kudin su babu matsala.

Abu yace kasashe irin su Saudi Arabiya da Ingila, ba sa bada wa’adi idan za su sauya kudi.

Shi kuwa masanin tattalin arziki na kasa da kasa Shuaibu Idris Mikati cewa ya yi, sauya kudin abu ne mai kyau amma shi ma ya yi suka akan wa’adin da aka sa na canjin kudi a bankuna da kuma yadda zai shafi talakawan kasa.

Mikati ya ce ana ganin kaman gwamnati ba ta damu da halin da talaka zai shiga ba, saboda haka ana musguna masu ne kawai. Ya kuma yi kira da a kai zuciya nesa.

Majalisar Dokokin kasa ta kara sa baki, inda ta roki Babban Bankin ya kara wa’adin zuwa 30 ga watan Yuli na wannan shekara da muke ciki.

Abin jira a gani shi ne ko mahukunta za su saurari koken al’umma wajen biya masu bukatar kara wa’adin canji kudin.

Saurari rahoton cikin sauti:Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like