Babban Dan Adawar Buhari Fayosr Zai bar Jam’iyyar PDP


Gogan caccakar manufofin gwamnatin Janar Muhammadu Buhari, Gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose ya nuna alamar zai iya barin Jam’iyyar PDP zuwa wata Jam’iyyar domin kara neman takarar Gwamna a karo na biyu. 

A cewar sa, “Ban san Jam’iyyar da zan yi amfani da ita a zaben 2019 ba, amma idan lokaci yayi zan sanar. Muna nazari akan batun. Dole mu buga dama mu buga hagu mu kuma buga tsakiya, duk Jam’iyyar da za mu dauko za ku sani”.

You may also like