A kokarin gwamnati na ganin ta kubutar da ‘yan matan makarantar Dapchi daga komar kungiyar Boko Haram, a jiya Talata shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umurci babban hafsan Sojin saman Nijeriya, Air Marshal Sadik Abubakar, ya koma jihohin Borno da Yobe domin cigaba da farautar ‘yan matan.
Kawo yanzu, rundunar sojan saman Nijeriya ta girke manyan jiragen saman yaki tare da kayayyakin aiki domin farautar ‘yan makarantar. Jiragen yakin wanda suke tashi daga birnin Maiduguri suna shawagi a sararin samaniyar hanyoyi da dajukan da suka hada birnin Maiduguri da jihar Yobe.
Babban hafsan sojin saman na Nijeriya, ya sha alwashin cewar dakarunsa za su yi aiki tukuru ba dare ba rana domin ganin sun kubutar da yara ‘yan makarantar daga hannun kungiyar Boko Haram.