Wani babban ɗan ƙungiyar Boko Haram mai suna Bulama Kailani Mohammad Metele ya miƙa kansa ga bataliyar soji ta 145,birged ta 5 dake garin Damasak na jihar Yobe.
Mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya Sani Usman ya bayyana haka yau a Maiduguri.
Yace Metele ya fito ne daga garin Tumbun Bera dake jihar Borno, na ɗaya daga cikin ƴan ƙungiyar ta Boko Haram ɓangaren Mamman Nur ƙarƙashin jagorancin Abu Mustapha.
Metele shine mai namba ta 253 a jerin sunayen da rundunar ta fitar na waɗanda take nema ruwa a jallo a kwanakin baya.
” Yanzu yana can ana cigaba da yimasa tambayoyi”yace
A wani bangaren kuma Usman yace sojojin bataliya ta 145 sun kama wasu mutane biyu da ake zarginsu da kasancewa yan Ƙungiyar ta Boko Haram, lokacin da suke yin leƙen asiri kan ƙauyukan Kareto da Dangalti bayan an samu bayanan sirri akansu.
Yace binciken farko yanuna cewa mutanen na shirya yadda za akai hari kan ƙauyukan.