Babban Sakataren OPEC Na Ziyara A Tehran


 

Babban sakataren kungiyar kasashe masu fitar da danyen man fetur a kasuwanninsa na duniya Muhammadu Barkindo ya iso birnin Tehran a jiya domin ganawa da jami’an gwamnatin kasar Iran kan zama na da kungiyar za ta gudanar.

A lokacin da yake ganawa da ministan mai na kasar Iran BIjan Zangine a yammacin jiya a Tehran, bangarorin biyu sun tattauna muhimman batutuwa da suka shafi batun faduwar farashin mai da kuma yadda za a farfado da shi.

Ministan na Iran na ya ce ga dukaknin alamu kasashen an OPEC za su cimma matsaya a zaman da za su gudanara  karshen wannan wata a birnin Geneva na kasar Switzerland, dangane da hanyoyin farfado da farashin mai a kasuwanninsa na duniya.

Idan har kasar ta Iran ta amince da ta rage yawan adaddin gangunan man da take hakowa, kamar yadda sauran kasashe mambobi a kungiyar suka amince da hakan, to kuwa hakan zai tasiri wajen daga farashin danyen man fetur a kasuwaninsa na duniya.

You may also like