Babban Sifetan yan sanda ya bayyana gaban kwamitin majalisar dattawa


Ibrahim Idris babban sifetan yan sanda na kasa ya bayyana gaban kwamitin wucin gadi na majalisar dattawa dake binciken wasu zarge-zarge da ake masa.

Majalisar dattawa ta kafa wani kwamitin wucin gadi ranar 4 ga watan Oktoba bayan da sanata Isa Hamma Misau ya zargi babban sifetan da aikata ba wasu laifuka.

Sanatan ya zargi babban sifetan da laifin karɓar kuɗi ba bisa ka’ida ba daga kamfanonin hakar man fetur inda aka tura jami’an yan sanda suyi aikin samar da tsaro.

Misau  ya kuma yi zargin cewa babban sifetan yana neman wasu yan sanda mata biyu inda yayi musu karin girma na musamman.

A ranar Larabar makon da ya gabata, kwamitin da Francis Alimikhena yake jagoranta yayi barazanar bada sammacin Idris bayan da ya gaza bayyana a gaban kwamitin.

Amma a ranar juma’a babban sifetan ya bayyana cewa zai girmama gayyatar da kwamitin yayi masa.

You may also like