Babban sifetan yan sanda ya gana da Osinbajo kan gayyatar da aka yi wa Saraki


Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo a ranar Litinin ya gana da babban sifetan yan sanda, Ibrahim Idris, da kuma shugaban hukumar tsaro ta farin kaya DSS, Lawan Daura a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Wata majiya ta shedawa jaridar The Cable cewa ganawar na da nasaba da rikicin dake faruwa tsakanin rundunar yan sanda da kuma shugaban majalisar dattawa Abubakar Bukola Saraki.

Rundunar yan sanda ta gayyaci Saraki domin ya amsa tambayoyi bayan da mutanen da aka kama da laifin fashi da makami a jihar suka bayyana cewa su yaransa.

Rundunar yan sandan tana son tabbatar da zargin da ake cewa akwai alaka tsakanin mutanen da ake zargi da kuma saraki.

Ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnati Abubakar Malami na daga cikin mahalarta taron.

You may also like