Babban sifetan yan sanda ya mayar da Janga matsayinsa na kwamishinan yan sandan jihar Kogi


An sake mayar da,  Ali Janga, mukaminsa na kwamishinan yan sandan jihar Kogi, mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, ASP William Aya, shine ya tabbatar da haka.

Aya ya fadawa kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN, ranar Alhamis a Lokoja cewa Janga ya dawo ofishinsa ranar 3 ga watan Afirilu bisa umarnin babban sifetan yan sanda na kasa, Ibrahim Idris.

Ya ce an dawo da Janga bakin aikine bayan da ya cika wa’adin mako guda  da babban sifetan yan sanda  ya  bashi na  ya sake  kama masu laifin da suka tsere daga wani caji ofis din yan sanda dake jihar.

Mai magana da yawun rundunar ya tabbatar da cewa dukkanin mutane shida da suka samu nasarar tserewa daga hannun yan sanda a ranar 28 ga watan Maris  an sake kama su.

Aya ya kara da cewa mutane 13 da suka taimaka musu wajen tserewa suma sun shiga hannun jami’an tsaro a Lokoja.

A cewarsa wadanda aka kama sun hada da wani mai hayar babur mai kafa uku wanda ya dauki mutanen ya zuwa maboya bayan da suka tsere da kuma mutumin da ya mallaki gidan da suka kwana bayan da suka gudu daga hannun yan sanda.

You may also like