Babban sifetan yan sanda yaki amsa gayyatar majalisar dattawa a karo na uku


Babban sifetan yan sanda Ibrahim Idris ya gaza bayyana gaban majalisar dattawa a karo na uku.

An sa ran Idris zai bayyana a gaban majalisar yau kan matsalar rashin tsaro da take kara ta’azzara a sassan kasarnan da kuma batun Dino Melaye sanata mai wakiltar mazabar Kogi ta tsakiya.

A karon farko da majalisar ta gayyace shi babban sifetan ya raka shugaban kasa Muhammad Buhari jihar Bauchi a ziyarar aiki da yakai.

A karo na biyu da aka sa ran zai bayyana gaban majalisar babban sifetan ya kai ziyarar aiki jihar Kaduna inda ya ziyarci garin birnin Gwari.

Bayan da aka tabbatar baya harabar majalisar a ranar Laraba, shugaban majalisar Bukola Saraki ya ce ya kamata a yanke shawarar matakin da za a dauka anan gaba.

Ba’a san dalilin da ya hana babban sifetan bayyana gaban majalisar ba.

You may also like