Babbar Kotun Tarayya Dake Abuja Ta Bada Umurnin A Saki Shaikh Zakzaky Daga Yau Zuwa Kwanaki 45, Sannan A Biya Shi Diyyar Naira Miliyan 25 Na Tsare Shi Ba Tare Da Bin Ka’ida Ba.
Wata kotun tarayya da ke birnin Abuja ta umarci hukumomin tsaro da su saki shugaban kungiyar Islamic Movement of Nigeria ta ‘yan Shi’a Sheikh Ibrahim El-zakzaky.
Kotun ta bukaci a saki El-zakzaky nan da kwanaki 45 ba tare da wani sharadi ba.
Alkalin kotun Kolawale Gabriel ya ce tsarewar da hukumomi ke cigaba da yi wa El-zakzaky tun watan Disamban bara haramtacciya ce kuma ba ta da hujja a karkashin dokokin kasar.
Haka ma ya umarci hukumomin da su biya shi da matarsa kudi Naira miliyan 50 a matsayin kudin fansa na tsare sun da aka yi a haramce.
A shekarar da ta gabata ne dai sojojin Nijeriya suka kama shugaban ‘yan Shi’ar bayan wata arangama da magoya bayansa a Zaria da ke arewacin kasar.
Akalla magoya bayansa 349 jami’an tsaro suka kashe a lokacin tarzomar.
Kungiyoyin kare hakkin bil’adama na gida da waje sun yi Allah-wadai da lamarin, sai dai sojojin sun kare matakin da suka dauka