Babbar Manufar Kasafin Kudin Jihar Gombe Ta 2018 – Dankwambo Gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo ya bayyana cewa jihar ta tsara kashe Naira Bilyan 104.9 a kasafin kudin 2018 don harkokin Jin dadin al’ummar jihar.

Ya ce, gwamnatin jihar za ta kashe sama da Bilyan 52 wajen gudanar da manyan ayyukan raya kasa sai kuma sama da Naira Bilyan 51 wanda aka tsara kashewa wajen harkokin yau da kullum inda ya jaddada cewa an tsara kasafin kudin ne ta hanyar la’akari da yanayin kuncin tattalin arzikin da aka fuskanta a cikin wannan shekarar.

You may also like