Babbar mota ta markade wasu mutane biyu har lahira akan hanyar Abuja zuwa Lokoja


Mutane biyu, wani direban babbar mota ya  markade har lahira a daren ranar Lahadi a kauyen Gada Biyu dake kan hanyar Abuja zuwa Lokoja.

Wani shedar gani da ido ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 9:12 na dare lokacin da wata babbar mota dake tahowa daga Lokoja ta bi takan mutanen biyu wadanda su ke kan babur.

Ya ce mai babur din da kuma mutumin da ya dauko suna tsallaka babban titin ne lokacin da motar ta kade su kuma  ta yi gaba ba tare da direban ya tsaya ba.

“Kafin mutane su karasa wurin tuni direban ya gudu.Amma kuma jami’an hukumar kiyaye afkuwar haɗura ta kasa FRSC sun kwashe gawarwakin ya zuwa Asibiti,” ya ce.

Da jaridar Daily Trust ta tuntubi kwamandan FRSC mai lura da yankin Abaji ACC Olasupo Esuruoso, ya tabbatar da faruwar hatsarin da ya alakanta da direba masu kade mutane su gudu.

You may also like