Babbar Sallah: Gwamnan Kaduna Ya Nemi A Zauna Lafiya


elrufai

 

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai ya yi kira ga al’ummar kasar nan, musamman na jihar Kaduna da su zauna da juna tafiya da kuma tausaya wa juna. Gwamnan ya yi wannan kira ne a sakonsa babbar Sallah da ya aike wa al’ummar musulmin jihar.

Gwamnan ya kuma nemi ‘yan Nijeriya da da su koma ga Allah, kuma su ci gaba da hakuri da halin kuncin da ake ciki a wannan lokaci, kuma su yi aiki tare don ganin an yi nasarar ceto  kasar nan daga halin da take ciki.

Gwamnan ya ce, “ina farin cikin taya al’ummarmu murnar babbar Sallah, da fatan Allah ya amshi sadaukarwarmu. Ina fatan za mu yi amfani da darussan da wannan Sallah ke kowar da mu. A wannan lokaci da muke ciki na kunci, ya kamata mu yi imani da kuma sadaukarwa don mayar da komai cikin tsari. Saboda haka ya kamata mu ci gaba da sadaukarwa.”

Ya ci gaba da cewa, “dole mu yi watsi da ‘yan ba-ni-na-iya, masu hada mu fada da juna saboda bambancin addini ko harshe. Ya kamata mu Sanya zaman lafiya a dukkan huldodinmu da juna. Mu zauna lafiya da juna ba tare da neman tada fitina ba.”

You may also like