Gwamnan jihar Imo dake a shiyyar kudu maso gabashin Nijeriya kuma shugaban gwamnonin jam’iyyar APC mai mulki Rochas Okorocha ya bayyana cewa dole ne duk wani dan siyasa a Nijeriya ya yi sata sannan ya rayu saboda albashin su ba wani mai yawa ba ne.
Gwamnan wanda ya bayyana hakan a lokacin da yake hira da wakilin gidan talabijin din nan mai zaman kansa na Channels ya bayyana cewa albashin gwamna a Nijeriya Naira dubu dari bakwai ne kacal kuma ba ya isar su.
Gwamnan ya kuma kara da cewa don haka dole dukkan wani dan siyasar da bashi da wata kwakkwarar sana’a da yake samun kudi banda albashin sa sai dai ya yi sata.