Babu barayi a jam’iyar APC – Osinbajo


Mataimakin shugaban kasa,Yemi Osinbajo, ya ce mambobin jam’iyar APC ba barayi bane.

Osinbajo, ya bayyana haka lokacin da yake lura da yadda zaben shugabannin mazabu na jam’iyar APC ke gudana a karamar hukumar Eti Osa dake jihar Lagos.

Mataimakin shugaban kasar yace gwamnatin jam’iyar APC ta banbanta da kowacce irin gwamnati da akayi a baya.

“Ta bangaren cigaba, duk abin da muka yi dole ya zama fitacce, makarantun mu asibitoci da kuma tituna dole su zama masu kyau da inganci. Saboda haka dole mu saka kudade. kuma za mu iya yin haka tabbas zai iya yiwuwa,”ya ce.

“Kamar yadda nake fada,a duk inda naje a fadin kasarnan, banbancin dake tsakaninmu da kuma kowacce irin gwamnati shine mu ba zamu saci kudi ba dole mu kasance muna da kwarin gwiwa.

“Mun fito ne mu dubaduba yadda abubuwa suke gudana, muji labari mai dadi cewa dukkanin zabukan shugabannin mazabu suna tafiya lafiya ba tare da tashin rikici ba ko kuma matsala, muna da kwarin gwiwa akan jam’iyarmu, dalilin da yasa muke da kwarin gwiwa shine mu ba barayi bane, mu na daban ne muna so ne mu bautawa jama’a kuma mutane ma sun san muna so mu bauta musu.”

A ranar Asabar ne dai aka gudanar da zaben shugabannin jam’iyar ta APC a matakin mazabu gabanin babban taron zaÉ“en shugabannin jam’iyar na kasa da za gudanar cikin watan Yuni.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like