‘Yan Nijeriya da dama sun yi Allah wadai da kiran da tsoffin shugabannin kamfanin NNPC suka yi na cewar, a cire tsayayyen farashin man Fetur, a bar kasuwa ta kayyade farashi na gaskiya.
Wannan dai na daga cikin shawarwari da dama da tsoffin shugabannin kamfanin NNPC suka bayar a taron da suka yi da shugaban kamfanin Dr Maikanti Baru.
Tuni aka fara fargaban cewa za’a iya kara farashin man, sai dai gwamnatin tarayya ta ce babu kanshin gaskiya a wannan magana.
Wannan batu ya fito daga bakin ministan man fetur Dr Ibe Kachikwu a yayin da ya ke yi wa manema labarai magana bayan ganawar da ya yi da shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Haka shi ma kamfanin na NNPC ya bayyana cewa tsoffin shugabannin sun bayyana ra’ayinsu ne kawai ba shawara suka bayar ba na a kara farashin man. Haka kuma kamfanin ya ce bashi da hurumin kara farashin mai ko kuma rage shi.