Babu Dalilin Bada Hakurin Dakatarwar Da Akayi Mini-Sanata Ndume Dakataccen Dan majalisar dattawa dake wakiltar mazabar kudancin Borno, Sanata Ali Ndume, yace bazai bada hakuri ba domin a dawo dashi majalisar. 

Bayan wata ganawa da yayi da mutanen mazabarsa a ranar lahadi, ya fadawa manema labarai cewa babu dalilin daza a nemi ya bada hakuri tunda dai baiyi wani abun laifi ba da ya jawo aka dakatar dashi daga majalisar. 

Majalisar ta dakatar da Ndume tsawon watanni shida bayan da majalisar tace dagangan ya kawo kudirin da zai batawa majalisar suna.

 Sanatan dai ya ankarar da majalisar kan zargin da akewa shugaban majalisar  Bukola Saraki na siyan wasu motoci masu tsada batare da biyan kudin fiton kwastam ba da kuma batun takardun karatun Sanata Dino Melaye.  

Bayan dakatarwar ne Sanata Dino Melaye ya nemi Ndume da yabawa majalisar hakuri domin a rage masa watanni ko kuma ma a janye hukuncin  da akayi masa .

Amma Ndume yace wannan ba zabi bane.
 


Like it? Share with your friends!

0

You may also like