Babu dan Najeriya da zai iya kayar da Buhari a 2019- Gundiri


Wani ƙusa a jam’iyar APC a jihar Adamawa, Injiniya Marcus Gundiri ya ce jam’iya mai mulki a jihar kullum kara karfi take bayan ficewar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar.
Ya ce babu wani dan Najeriya da zai takara da shugaban kasa Muhammad Buhari a shekarar 2019 saboda nasarar da ya cimma da kuma farin jininsa.

“Waye kuma a yan zu cikin  kasarnan zai iya tsayawa zaɓe da Buhari kuma yayi nasara? bana jin akwai wani,” Gundiri ya fadi haka a matsayin martani kan tambayar da aka yi masa kan yiyuwar  sake zaɓen Buhari a shekarar 2019.

Ya kara da cewa, ” idan ka kalli nasarar da wannan shugaban ƙasar ya samu cikin yan shekarun nan sai da PDP suka shafe shekara 16 kafin su kafa tsarinsu baza kayi tsammanin jam’iyar APC cikin shekara 3  ta iya kafa irin wannan tsarin dole sai an dauki lokaci.

” idan kabawa shugaban kasa ƙarin wasu shekara huɗu zai yi abin kwarai sosai fiye da yadda PDP tayi cikin shekaru 16. Kalli, Buhari ya shiga gwamnati ne lokacin da kasarnan take cikin wani mawuyacin hali; tattalin arziki tsaro da kuma dukkanin matsaloli dake da alaƙa da shugabanci.”

Gundiri wanda ya fadi haka a Abuja lokacin da yake amsa tambayoyi daga yan jarida ya bayyana cewa ficewar Atiku daga jam’iyyar ba zai kawo wani gagarumin sauyi ba.

You may also like