Babu hujja ko daya game da badakalar Sarkozy a Libya


 

Kwamitin bincike kan laifukan da tsohon shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy ya aikata a kasar Libya ya sanarwar da ce babu wata kwakkwarar hujja game da tuhume-tuhumen da aka yi masa.

A tsakiyar watan Maris na shekarar 2011, a daidai lokacin da Libya ta rikice kana kuma Faransa ta mara wa masu adawa gwamnatin marigayi Gaddafi baya,sai daya daga cikin ‘ya ‘yan tsohon shugaban Libya wato Saiful Islam ya fito a gaban kafar yada labarai ta Euronews,inda ya bukaci da Sarkozy ya dawo da kudin da gyatuminsa ya ba shi.

Watanni 12 da afkuwar wannan lamarin, a sa’ilin da Sarkozy ya fadi a yakin neman zaben shugabancin kasar Faransa na 2, sai Mediapart ta wallafa wasu takardu masu dauke da sa hannun shugaban jami’an leken asirin Libya Musa Kusa,wadanda ke nuna cewa Muhammad Gaddafi ya tallafa Sarkozy da zunzurutun kudi yuro milyan 50 a lokacin kamfen.

Duk da yawan shaidun da ake su a kasashen Libya da Faransa game wannan batun,amma alkalai na ci gaba da cewa banda maganganu baki babu wata kwakkwarar hujja za ta sa a hukunta Sarkozy.

You may also like