Babu ja da baya kan dokar hana kiwo a jihar Benue- Ortom


Samuel Ortom gwamnan jihar Benue yace fulani makiyaya sun fadi ƙasa wanwar idan kisan baya bayannan suna yinsa ne domin tilasta gwamnatinsa gyara dokar hana kiwon shanu a fili.

Dokar wacce ta ƙunshi hana kiwon dabbobi ciki har da tafiya da su ana korasu ƙasa  a ko ina cikin fadin jihar.

Da yake kare matakin da ya ɗauka a wurin taron jana’izar mutane 73 da suka rasa rayukansu a hare-haren da ake zargin Fulani makiyaya da kaiwa wanda aka  gudanar a Makurdi ranar Alhamis, Ortom jaddada cewa killace dabbobi wuri guda shine hanyar kiwo ta zamani da yakamata abi kuma itace hanyar da  sauran al’ummar duniya da suka cigaba ke amfani da ita.

Ya kuma dora alhakin kisan kan shirun da gwamnatin tarayya tayi.

Gwamnan ya koka kan cewa da gwamnatin tarayya tayi aiki da rahoton da ya miƙa mata kan barazanar da kungiyar fulani ta Miyetti Allah Kautal Hore tayi, da za a iya hana kisan mutanen.

Ya shawarci gwamnatin tarayya kan ta kama shugabanin ƙungiyar Miyetti Allah Kautal Hore.

You may also like