Babu ja da baya wajen jinginar da kamfanin sarrafa karfe na Ajaokuta -Gwamnatin Tarayya 


Gwamnatin tarayya ta ce baza ta sake kashe ko sisin kwabo ba  a kamfanin sarrafa karfe na Ajaokuta dake jihar Kogi.

Kayode Fayemi, ministan ma’adanai da kuma sarrafa karafa ya bayyana haka a wurin wani taron manema labarai a Abuja.

Ya ce gwamnatin za ta cigaba da shirin jinginar da kamfanin, yinkurin da majalisar wakilai ba ta yi na’am da shi ba.

Yakubu Dogara, shugaban majalisar ya ce yan majalisar za su bijirewa shirin jinginar da kamfanin da ya bayyana a matsayin “asarar” dala biliyan $5.1 da aka ce an kashe wajen samar da shi.

Amma Fayemi ya dage kan cewa babu ja da baya wajen jinginar da kamfanin.

Fayemi, ya ce a kasafin kudi na shekarar 2017 ma’aikatar ta nuna cewa “jinginar da kamfanin Ajaokuta” kuma majalisun kasa  suka amince a kashe biliyan ₦2
“Saboda haka abin ya zo mini da mamaki lokacin da naji abin da Dogara ya ce ba za a kyale bayar da jinginar ba. Abin da muka yi ka wai shi ne aiwatar da abin da suka amince da shi ya zama doka.”ya ce.

“Mun yarda cewa Najeriya ba za ta sake kashe ko dala daya ba kan karasa aikin.Mun kashe kusan dala biliyan $8 tun daga shekarar 1979 lokacin da aka fara aikin kamfanin.

You may also like