Babu Mai Iya Satar Kudaden da EFCC ta Kwato – Ribadu


ribaduhandup

 

Tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC Malam Nuhu Ribadu ya bayyana cewa babu yadda wani zai iya satar kudaden da aka kwato daga hannun barayin gwamnati.

Ya bayyana haka ne a jiya Litinin yayin da yake jawabinsa a taron makarantar Institute of Management a Babban birnin Tarayya Abuja.

Ribadu ya ce kudaden yanzu haka na hannun hukumar kuma ana ado ne kawai da su tunda baza’a iya taba su ba. Amma dole a karshe a tura su ga gwamnati.

 

Ribadu ya kuma bayyana cewa hakkin shugaban kasa ne ya yaki cin hanci da rashawa ta kowacce kafa kuma a kowacce jaha, sako da lungu na kasar nan, ba hakkin wani gwamna ko shugaban karamar hukuma ba.

Ya kuma yi kira da ‘yan Nijeriya da su rungumi wannan yaki da hannu biyu kuma a jimiri goyan bayan masu gaskiya a duk inda aka sansu, domin a kara karfafa masu gwiwa.

You may also like