FITATTUN MATA: Farfesa Fatima Batul Mukhtar


Farfesa-Fatima-Batulu-Mukhtar

 

‘Babu Maraya Sai Raggo’

FARFESA FATIMA BATULU MUKHTAR, tsayayyiyar mace marar wasa, kaifi daya a duk abin da ta fada. A Jami’ar Tarayya ta Dutse sukan kira ta da agogo sarkin aiki. Duk da Farfesa Fatima ta tashi cikin maraici wannan bai sa ta zauna ba tare da samarwa kanta kyakkyawar rayuwa ba, wannan ya kara tabbatar da cewar babu maraya sai raggo.

 

Tarihina

An haife ni a unguwar Marmara cikin birnin Kano. Mahaifina ya rasu tun ina karama a sanadiyyar hadarin jirgin sama a shekarar 1969, kafin ya rasu yana rike da mukamin Sakataren dindin a Kano.

Bayan rasuwar mahaifina sai kakanmu na wajen uba, Limamin Kano Dan Amu ya dauki nauyin rikonmu da tarbiyyarmu da kula da duk al’amuranmu ni da sauran ‘yan uwana.

Na yi makarantar furamare ta Shahuci. A lokacin tun daga Marmara har Shahuci a kafa nake zuwa, komai sanyi ko ruwa, amma da yake kakata jaruma ce, duk yanayi takan yi mana tanadin kayan sawa wadanda za su taimaka mana. Idan damina ce kuwa tana tanadar mana rigar ruwa da takalmin ruwa wannan ta sa rashin lafiya kadai ke hana mu zuwa makaranta.

Haka in mun dawo za mu tafi makarantar allo a unguwar Soron Dinki, da dare kuwa babu fashin zuwa Islamiyya a unguwar Daneji. Kasancewar gidanmu babba ne, duk Assabar da Lahadi malami ne musamman zai zo domin karantar da mu Alkur’ani, a nan muke hadda da wanke allo.

Da na kammala aji hudu sai aka mayar da ni makaranta furamaren kwana ta mata da ke Shekara, na kammala a shekarar 1975. Daga nan sai na wuce sakandare ta Dala, inda bayan na gama a shekarar 1980 na sami gurbin share fagen shiga jami’a a ABU Zari’a, inda na yi shekara daya daga nan na wuce Digiri na yi shekara uku, na fito da shaidata a hattama digiri a shekarar 1984.

Na fara aikin yi wa kasa hudima a Jihar Ondo, amma sai ‘yan uwa suka matsa lallai sai in dawo Kano mahaifata. Haka kuwa aka yi, na dawo Kano na ci gaba hidima har Allah ya sa na gama, cikin ikon Allah na samu miji aka yi min aure.

Lokaci guda kuma na samu aikin koyarwa a makarantar (CAS) ta Kano, da gurbin ci gaba da karatun digiri na biyu. So na da karatu ya sa na zabi mayar da hankali kan makaranta tare da barin aiki, na koma ABU, amma saboda wasu dalilai dole na sake komawa Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK). Bayan na kammala ne kuma na samu aiki a nan BUK, hakan ya ba ni damar a ci gaba da zurfafa karatuna kan ilmin fannin tsirrai watau (Botany).

Lokacin da aka yi tunanin kafa jami’ar North-West da ke Kano sai aka sanya ni cikin Kwamitin Tantancewa, bayan an kafa Jami’ar sai aka jefa ni Kwamitin Aiwatarwa, sai kuma aka nemi in zama Shugaba farko a Tsangayar Kimiyya ta Jami’ar domin ta kafu.

Bayan shekara biyu aka sake sabunta nade-naden mukamai a jami’ar, inda aka nada ni Mataimakiyar Shugabar Jami’ar. Ina rike da wannan matsayi ne kuma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada ni Shugabar Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke garin Dutse a Jihar Jigawa.

 

Gwagwarmayar Rayuwa

Tun tasowata gwagwarmayar neman ilimi ce a gabana, duk da na tashi gidan malamai na addinin Musulunci kuma cikin maraicin iyaye, amma wannan bai zama matsala a gare ni ba, na sami goyon baya cikakke wajen kakannina da sauran ‘yan uwa. Wannan ya haifar min da ci gaban da a kullum nake alfahari da shi, domin ya yanke dukkan shiri na zama malalaciya. Duk ayyukana ma fi yawa a cikin jami’a na yi su.

Na yi rubuce-rubuce da dama a bangarori daban-daban. A kullum burina in samu ci gaba, har ta kai ga na zama Farfesa cikin kankanin lokaci. Na shiga cikin kwamitoci masu yawan gaske. Na rike Ko’odineta a sashen da nake watau Kimiyya, da sauran fannoni daban-daban, har zuwa Shugabar Sashen Kimiyyar Tsirrai.

 

Shugabancin Jami’ar Tarayya Ta Dutse

Duk da na rike mukamai da dama a cikin jami’a, akwai bambanci da a damka jami’a sukutum a hannunka. Jami’ar sabuwa ce, amma ina iya bakin kokarina wajen ganin ta yi kafada da kafada da takwarorinta. Alhamdulillahi, za a iya cewa kwalliya tana biyan kudin sabulu.

 

Kalubale

Rayuwa dole cike take da kalubale ko dai a yi nasara ko kuma akasin haka. Babban kalubale da na fuskanta shi ne hada aure da karatu a lokaci daya; ga kula da maigida, yara, iyaye da ayyukan ofis. Kuma kowanne so ake yin a yi daidai gwargwardo. Hakika na fuskancin kalubale ta wannan bangaren.

Kasancewata mace wadda ke jagorantar maza da dama bai zamar min matsala ba, ina samun cikakken goyon baya daga magabatana domin gudanar da aikina kamar yadda kowa zai yi kullum. Wannan aiki amana ce a gare ni, kuma Allah zai tambaye ni yadda na yi da ita, saboda haka dole in zage damtse don sauke nauyin da yake wuyana.

 

Nasarori

Alhamdulillahi, na samu nasarori da dama. Na gina katafaren lambu na shakatawa (Kano Botanical Garden KBG), wanda ke hanyar Dawakin Kudu, ina alfahari da shi sosai, domin ya zama sansani na koyo da koyarwa wajen da dalibai kan samu ilimin muhimmancin tsirrai irin namu na gargajiya. Akwai ‘ya’yan itatuwa irin su Tsada da Kadanya da Dinya da Danya da Magarya da Kurna da sauransu. Na kawata wajen ne da tsirranmu na dauri saboda da dama yara masu tasowa ba su san su ba. Akwai kuma tsirrai na zamani. Kuma waje ne bayan nazari ana iya shirya tarurruka da bukukuwa da sauransu.

Na yi wani hobbasa na hada taro, inda likitoci da masu maganin gargajiya suka zo aka tattauna don fahimtar juna da kara wa juna sani.

Wata nasarar ita ce, ina iya tsara da fitar da taswirar wuraren da ya kamata a shuka tsirrai da fulawowi a gidaje, domin da yawa suna yin gaban kansu ne, ba su san inda ya dace su dasa iri ba.

Haka zalika ina kula wa mutane da shuke-shukensu ta hanyar bibiyar lafiyarsu da tsarin da ya dace da su.

A matakin Jami’ar da nake shugabanta a halin yanzu, nasara ba ta yiwuwa sai da tallafi, saboda haka ma Bahaushe yake cewa, hannu daya ba ya daukar jinka. Nasarorin da na samu na da nasaba da goyon baya da jigogin makarantar suka rika nuna min, babu wanda yake wulakanta ni ko yi min katsalandan a aikina; ba wanda ke kallon na a matsayin mace indai a batun aiki ne.

A bangaren masarautun Jigawa akwai fahimta da girmamawa tsakaninmu, sun kawo min ziyara tare da nuna goyon baya.

Duk da cewa jami’ar ta Tarayya ce, amma hakan bai hana Gwamnatin Jihar Jigawa nuna min goyon baya na musamman ba, suna ba ni kulawa sosai, da zarar mun bukaci ganin Gwamna idan wata matsala ta taso, ba ma  shan wahala, take yake sauraronmu.

Ya wajibi ne gare ni in bayyana farin cikina bisa ayyukan ci gaba da Tsohon Shugaban Jami’ar ya kawo wa makarantar musamman ta fuskar gine-gine, da yardar Allah za mu dora daga inda ya tsaya.

 

Kirana Ga Mata

Kullum jajircewa ita ce matakin nasara. Haka zalika babu yadda mace da za ta taka matakan nasara sai da goyon bayan iyaye da mijintana aure. Ina alfahari da kakata wadda jajircewarta a tarbiya, kula da karatun da kula da lafiya ya kai ni ga ta taka kowanne matsayi a yau. Babban wanta Kabir Mukhtar ya taka rawar gani, ya maye gurbin uba. Da akwai ‘yan uwan iyaye musamman Alhaji Alfa Wali sun taimaka min matuka. Iyayen miji ma suna da ta su rawar takawa, domin sai sun dafa, idan suka kyamaci aikin zai yi wahala a sami nasarar da ake nema.

Aiki ga mace abu ne mai wahala amma idan mace ta tsara lokacinta na aiki da na maigida da na yara sai komai ya zo da sauki.

Iyaye su dage da yi wa yaransu addu’a su dage su dora yaran akan mizani na kwarai.

 

Fatana

Alhamdulillah yanzu babban burina da fatana shi ne tsira wajen Allah da dacewa duniya da lahira da samun sakamako na gidan aljanna.

Jami’ar Tarayya ta Dutse ta yi fice, ba wai cikin tsaranta ba, a’a, tana gogayya da jami’o’in ciki da wajen kasar nan. Haka su ma dalibanta sun yi zarra, ina da burin dora jami’ar kan mizani wanda ko bayana tarihin jami’ar ba zai manta da ni ba.

Tare da  Al-Amin Ciroma

 (08033225331)
ciroma14@yahoo.com

You may also like