Babu Sauran ‘Yan Boko Haram a Dajin Sambisa – Buhari


 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa dakarun sojin Nijeriya sun yi nasarar fatattakar sauran mayakan Boko Haram daga maboyarsu da ke dajin Sambisa.

Ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce dakarun sun cimma haka ne a ranar Juma’ar da ta gabata.

A bisa wannan ne shugaban ya ce ya na taya sojojin murna. A cewar sa, “ina so na yi amfani da wannan dama in yaba da jarunta da juriyar da dakarun rundunar Operation Lafiya Dole suka nuna, inda a karshe suka shiga, tare da cin karfin mayakan Boko Haram da suka yi saura”.

Shugaba Buhari ya ce, mayakan ba su da sauran mafaka ganin wannan shi ne wurin da ya rage musu kafin sojojin su fatattake su.

Dakarun sojin Nijeriya dai sun kwashi tsawon makonni a farmakin da suka kaddamar kan maboyar mayakan da ake ganin shi ne maboyarsu daya tilo da ya rage a dajin na Sambisa.

Sai dai kuma har yanzu mayakan kungiyar ta Boko Haram na kai hare-haren kunar bakin wake a arewa maso gabashin Nijeriya.

An yi kiyasin cewa kungiyar ta halaka fiye da mutane dubu goma sha biyar, da raba wasu mutanen fiye da miliyan biyu da matsugunninsu tun bayan bullowar kungiyar shekaru bakwai da suka wuce.

You may also like