
Asalin hoton, OTHER
Ƙungiyar Transparency International ta ce saɓanin yadda wasu suka ɗauka, babu wani abu da ya canza a yaƙin da Najeriya ke yi da cin hanci da rashawa, don kuwa har yanzu makinta bai wuce 24 ba.
Kungiyar ta ce matsayin Najeriya ya ɗaga ne a jerin ƙasashen duniya wajen yaƙi da cin hanci da rashawa ne zuwa mataki na 154, saboda wasu gyare-gyare na dokoki da ta yi.
Wakilin kungiyar a Najeriya, kuma darakta a Cibiyar Rajin Kyautata Ayyukan Majalisun Dokoki da Yaƙi da Rashawa a Najeriyar wato CISLAC Auwal Musa Rafsanjani, ya shaida wa BBC cewa gyaran da aka yi a dokar zaben kasar, ya taimaka wajen daga matsayin Najeriya.
Ya ce, “ Baya ga gyaran da aka samu a dokar zaben Najeriya, akwai wasu dokokin da ‘yan majalisar kasar ma suka zartar da su kuma shugaban kasa ya sanya hannu a kai, kamar misalin dokar halasta kudin haram, gyara a kan wannan doka ya kara fito da kimar Najeriya a idanun duniya.”
“Sai kuma dokar nan wadda majalisar ta yi kuma aka zartar ta idan an kwato kudin da aka sata a Najeriya za a yi amfani da su ta hanyar da ta dace, ita ma wannan doka ta yi tasiri sosai wajen kara fito da kimar Najeriya.”
Auwal Musa Rafsanjani, ya ce, yadda hukumomin yaki da cin hanci da rashawa ma suka yi kokari wajen tabbatar da sun rage duk wasu ayyukan cin hancin da ma kama wadanda suka aikata ba dai-dai ba, shi ma ya daɗa janyo martabar Najeriya.
Wakilin kungiyar ta Transparency International, ya ce to amma duk irin wannan kokari da aka yi, idan aka duba irin tabarar da aka yi ta rashin bincikar wadanda aka samu da aikata cin hanci da rashawa, za a ga cewa babu wani ci gaba da aka samu a yakin da ake da wannan mummunar dabi’a a kasar.
Ya ce, “Irin yadda ake aikata cin hanci a bangaren tsaro wato irin kudaden da aka warewa bangaren ma, ya sa matsalar tsaro na kara tabarbarewa bisa la’akari da yadda ake rasa rayuka da dukiyoyin al’umma.”
Auwal Musa Rafsanjani, ya ce, “A bangaren kudaden tallafin mai ma ana tafka badakala wato cuwa-cuwa, haka a bangaren aikin shari’a ma ana tafka cin hanci da rashawa saboda ana zargin hukumomin shari’a da aikata wannan ta’asa amma kuma ba wani abu da aka yi a kai.”
Wakilin kungiyar ta Transparency International din ya ce, da shugabannin Najeriya za su bude kunnuwansu su ji shawarwarin da ake ba su domin a kyautata yaki da cin hanci da rashawa, kuma a tabbata an toshe duk wasu hanyoyin da ake bi wajen sace arzikin kasa, da abubuwan sun inganta, maimakon yadda ake mayar da yakin batu na siyasa.