Babu shirin korar ma’aikata a jihar Bauchi – Liman Bello


Gwamnatin jihar Bauchi ta kawar da jita-jitar da ake yadawa cewa tana shirin korar wasu ma’aikatan jihar.

Shugaban ma’aikata na jihar Alhaji Liman Bello shi ne ya bayyana haka lokacin da yake tattaunawa da manema labarai.

Ya ce jita-jitar wasu mutane ne suke yaɗata domin bata sunan gwamnatin jihar.

Bello ya ce, gwamnati mai ci bata da shirin korar ko wane ma’aikaci inda ya ƙara da cewa jita-jitar wani bangare ne na ƙoƙarin da wasu yan jihar marasa kishi keyi na yin zagon kasa ga ƙoƙarin gwamnatin jihar na bunƙasa aikin gwamnati.

Shugaban ma’aikatan ya shawarci ma’aikatan da kuma mutanen jihar kan suyi watsi da jita-jitar domin gwamnati tana yin duk abinda ya dace wajen inganta aikin gwamnati da walwalar ma’aikata.

Da yake magana kan ma’aikatan wucin gadi, ya ce gwamnati ta yanke shawarar korar ma’aikatan ne saboda kwantiraginsu ya ƙare.

 

You may also like