Babu Tabbas Akan Batun Amfani Da Na’urar Tantancewa Wajen ZabeYa yin daya rage kasa da makonni hudu a gudanar da zaben shugabannin kananan hukumomi a jihar Jigawa, hukumar zabe ta jihar tace  har yanzu bata kai ga cimma matsaya ba kan zatayi amfani da na’urar tantance masu zabe ta card reader ba ko kuma a’a.

A ranar daya ga watan gobe na Yuli, ne dai hukumar zaben ta jihar Jigawa zata gudanar da zaben kananan hukumomin kamar yadda yakr kunshe a cikin jadawalin ta na zaben bana.

Jimular masu kada kuri’a miliyan guda da dubu dari tara ne suka yi rajistar zabe a fadin jihar ta Jigawa, kuma ana sa ran cewa sune zasu fito domin zaben shuwagabnin kananan hukumomi ashirin da bakwai da kuma kansiloli fiye da dari biyu a fadi jihar ta Jigawa.

Shugaban hukumar zaben jihar Jigawa Alhaji Muhammad Sani, yace shirye shiryen zabe sun kankama amma ya furta cewa har yanzu hukumar bata yanke shawara ba kan batun nau’rar tantance masu zabe watau “Card Reader” ba, wanda masu lura da al’amuran siyasa suka yi amannar cewa ta taka rawa wajen kyautatuwar zabe a shekarar 2015.

You may also like