Babu Wanda Ya Isa Ya Hana Ni Zama Shugaban Nijeriya A 2019 In Har Allah Ya Nufa-Sule Lamido


Tsohon Gawmnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido ya ce matukar Allah ya kaddara zai zama shugaban kasar Nijeriya, to babu wani mutum da ya isa ya hana komai karfinsa.
Lamido wanda ya ke magana da manema labarai ya nuna bacin ransa kan bisa yadda gungun ‘yan sanda suka hana magoya bayansa yin taron nuna goyon bayansa a garinsa na Bamaina.
Tsohon Gwamnan ya ce shi bai taba ganin inda aka ce wai sai ka nemi izini kafin ka yi taro kai da masoyanka ba.
“Ubangijin da ya bai wa Tafawa-Balewa, Ironsi, Gowon, Murtala, Shagari, Buhari, Babangida da Jonathan mulki, shi zai bani idan ya ga dama. Don haka babu wani tasiri da karfi ko cin zali za su yi a kaina.

You may also like