Babu Wanda Ya Rayu Cikin Hatsarin Jirgin Saman Soje Kasar Rasha A Safiyar Yau Lahadi


4bkc2f46ed5548jzhy_800c450

Majiyar labarai daga kasar Rasha sun bayyana cewa wani jirgin saman sojen kasar dauke da mutane 91 ya yi hatsari ya kuma fada a cikin tekun Black Sea a safiyar yau ya kuma kashe dukkan mutane 92 da suke cikin jirgin

Kamfanin dillancin labaran Sportmic ya bada labarin cewa an birnin jin doriyar jirgin ne mintuna 20 bayan tashinsa daga tashar jiragen sama na Suuchi.  A halin yanzu dai jami’an bada cheton gaggawa sun garzaya zuwa bakin tekun Black sea inda suka gano mitoci 50-*70 karkashin ruwa kuma dukkan fasinjojin jirgin sun mutu .

Labarin yan kara da cewa jirgin saman samfurin TU-154 yana kan hanyarsa ta zuwa birnin Lazikiyya na kasar Siria ne kuma 8 daga cikin mutane 91 da yake dauke da su ma’aikatan jirgin ne a yayinsa sauran 83 sun hada da jami’an sojojin kasar, yan jaridu, masana a bangarori daban daban.

Labarin ya kammala da cewa mai yuwa matsalar na’uroti ne jirgin ya samu ko kuma kuskuren matuki.

You may also like