Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya ce bashi dan takara da yake goyon baya a zaɓe mai zuwa .
Obasanjo ya bayyana haka ranar Laraba lokacin da wata kungiyar matasa daga jihar Delta, Ƙarƙashin shugabancin, Frank Esanubi mai neman takarar gwamna suka kai masa ziyara a gidansa dake Abeokuta,jihar Ogun.
Da yake wa matasan jawabi Obasanjo yace matakin da ya ɗauka na ƙauracewa harkokin jam’iyun siyasa har yanzu yana nan.
A shekarar 2015 tsohon shugaban ƙasar ya bada sanarwar dai na shiga harkokin jam’iyun siyasa.
“A shekarar 2015 na ce bazan kara shiga harkokin jam’iyun siyasa ba har kuma yanzu ina kan matsayina,” ya ce.
“Kowa da kowa ba tare da duban jam’iyar da yake ba zai iya zuwa wurina neman shawara zan yi farin cikin yin haka.
“Bani da wani dan takara ko wane iri ne dake neman ɗarewa wata kujerar siyasa kawai na yarda cewa dole ne sai a gudanar da abubuwa ta hanya mai kyau domin samun kyakkyawan sakamako.”